Najeriya ta samu cigaba a bangaren noma – Bagudu

Najeriya ta samu cigaba a bangaren noma – Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu ya ce Najeriya na samun cigaba mai tarin yawa a bangaren harkokin da suka shafi noma.

Da yake jawabi a Damaturu wurin wani taro na musamman da gwamnatin jihar Yobe ta shirya, Gwamnan ya ce a cikin shekaru biyar da suka wuce gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo cigaba cikin harkokin noma.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Wani babban jami'in dan sanda ya rasu a Sokoto

“Gwamnatin Buhari ta kashe sama da naira biliyan 200 domin bada bashi ga manoma cikin tsarin ABP domin samar da yalwataccen abinci.” Inji Gwamnan.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka samu wannan rance da suyi amfani da shi ta hanyar da ya dace domin taimakon gwamnati kamar yadda ake bukata da wajensu.

“Mun kai tsawon lokaci a kasar nan bamu iya ciyar da kanmu, ba wai don ba za mu iya ba saboda da kawai halin rashin kulawa ne. Amma tun daga lokaci da Shugaba Buhari ya hau mulki sai labarin ya canja.

“Ka da kuma mu manta, noma kamar yadda sauran kasuwanci suke, ana iya samun asara cikinsa. A don haka idan wannan ya same mu kar mu damu idan bamu ci riba ba a yau gobe ma ran ace.” Inji Bagudu.

Bagudu ya kara da cewa, akwai lokacin da gwamnatin Najeriya ta taba ware zunzurutun kudi har tiriliyan 7 domin ceto bankunan daga shiga halin tsaka mai wuya. “Idan har gwamnati za ta iya kashe irin wannan kudi saboda bankuna, me yasa ba za a kashe tiriliyan daya kadai ba domin bunkasa noma?” Gwamnan ya yi tambaya.

A karshe ya yiwa jihar Yobe addu’a da fatan jihar ta kasance cikin jihohin da suka samu bunkasa a bangaren noma a kasar nan.

https://www.dailytrust.com.ng/nigeria-making-progress-in-agriculture-gov-bagudu.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel