Nan da shekara 15 man fetur zai zama 'kayan kawai' - Gwamna Badaru

Nan da shekara 15 man fetur zai zama 'kayan kawai' - Gwamna Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Dakta Muhammadu Badaru Abubakar ya ce man fetur zai rasa darajarsa nan da shekaru 15 masu zuwa.

A jawabin da gwamnan ya yi wurin taron aikin noma a Damaturu, ya ce dole Najeriya ta dena dogaro ga man fetur a matsayin babban abinda ke samar mata kudin shiga idan tana son ta cigaba da zama da kafar ta.

Ya yi hasashen cewa nan da shekaru 15 man fetur ba zai yi daraja ba a kasuwani duba da irin cigaba na fasaha da ake samu a kasashen duniya.

DUBA WANNAN: Wata mace musulma bakar fata ta sake lashe zabe a Amurka

Badaru ya yi nadamar cewa duk da irin albarkatun da Allah ya bawa Najeriya, kasar ta dogar da man fetur na lokaci mai tsawo wadda hakan na kawo cikas ga sauran bangarorin tattalin arziki.

Ya shawarci jihar Yobe ta mayar da hankali kan noman Ridi da Karo wadda a cewarsa jihar ce ke noma mafi kyawu da ake nema a kasuwanni.

Gwamnan ya kuma gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda bullo da shirinsa na 'Mu koma gona' da ke karfafa wa al'umma gwiwa domin su rungumi noma a matsayin sana'ar da za ta ba su 'yanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel