Yanzu-yanzu: Wani babban jami'in dan sanda ya rasu a Sokoto

Yanzu-yanzu: Wani babban jami'in dan sanda ya rasu a Sokoto

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da tantance sabbin 'yan sanda da za a dauka a jihar Sokoto, Suleiman Zubairu, ya rasu.

Ya rasu ne a safiyar ranar Litinin yayin da ya ke shirin barin masaukinsa a hanyarsa na koma wa Abuja bayan ya kammala aikinsa a jihar ta Sokoto.

Mai magana da yawun 'yan sanda na jihar Sokoto, DSP Muhammad Sadiq ya tabbatar da afkuwar rasuwar inda ya ce ACP Zubairu yana shirin baro gidansa domin koma wa Abuja ne yayin da ya rasu.

"Ya kammala aikinsa a jihar Sokoto domin an kammala aikin tantance sabbin 'yan sanda da za a dauka ranar Asabar," inji shi.

DUBA WANNAN: Wata mace musulma bakar fata ta sake lashe zabe a Amurka

Ya kara da cewa: "Bai sanar da kowa cewa ba shi da lafiya ba. Lafiyarsa kalau. Mutuwarsa ya razana mu."

Daily Trust ta ruwaito cewa iyalan mammacin za su zo Sokoto inda ake sa ran za a binne shi.

Babban limamin masallacin Juma'a na Abu Huraira, Dakta Mansur Ibrahim ya sanar a shafinsa na Facebook cewa za ayi jana'izar mammacin a masallacin a ranar Talata.

Ya bukaci musulmi da ke yankin su hallarci jana'izar da za ayi misalin karfe 9 na safe.

Ya yi addu'ar Allah ya jikan mammacin ya gafarta masa.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa mammacin dan asalin jihar Adamawa ne da ke aiki a hedkwatan 'yan sanda a Abuja kafin aka aike da shi aikin wucin gadi na tantance sabbin masu son shiga aikin 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel