Mataimakin gwamnan Kogi ya maka gwamnan jihar a kotu

Mataimakin gwamnan Kogi ya maka gwamnan jihar a kotu

Rahotanni sun kawo cewa mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Simon Achuba, ya shigar da karar Gwamna Yahaya Bello na jihar a gaban Kotu. Har ila yau Achuba ya maka Kwamishinan Shari’a na jihar ma a gaban kotu.

Mataimakin gwamnan ya yi kararsu ne saboda neman a biya shi hakkin sa na alawus-alawus da ya ce gwamnan ya ki ba shi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

A cikin takardar kara mai lamba NICN/ABJ/244/2019 da aka shigar a ranar 19 ga watan Agusta, Achuba ya roki kotun cewa hana shi alawus din da gwamna Bello ya yi na tsawon lokaci, nuna bambanci ne,da kuma rashin adalci.

Hakazalika mataimakin gwamnan ya bukaci kotu ta sa a biya shi naira miliyan 921.5 a matsayin wasu kudaden sa na alawus din tafiye-tafiye da gwamnan ya ki ba shi.

Sannan akwai wasu alawus na mako-mako, kudaden gudanar da tsaro a matsayin sa Mataimakin Gwamna da su ma suka wajaba a rika ba shi, amma duk ba a ba shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An ba hukumar NCC wa’adin kwanaki 10 domin ta toshe layuka miliyan 2

Idan za ku tuna a cikin watan Fabrairu nne dai Achuba ya ce rayuwar sa na cikin hatsari, domin gwamna ya sa an janye jami’an tsaron da ke kare lafiyar sa.

Cikin watan Agusta kuma Majalisar Jihar Kogi ta fara wani yunkuri na tsige Achuba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel