Yanzu Yanzu: An ba hukumar NCC wa’adin kwanaki 10 domin ta toshe layuka miliyan 2

Yanzu Yanzu: An ba hukumar NCC wa’adin kwanaki 10 domin ta toshe layuka miliyan 2

Gwamnatin tarayya ta ba hukumar kula da ma’aikatun sadarwa ta kasa (NCC) wa’adin ranar 25 ga watan Satumba, domin ta datse layukan waya miliyan 2.242 da ba a yiwa rijista ba a kasar.

Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ne ya bayar da umurnin a ofishinsa da ke Abuja a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba.

“Ina da labari da dumi-dumi zuwa gare ku: bayan sanarwar da nayi a makon da ya gabata game da layukan waya miliyan 9.2, mataimakin shugaban hukumar NCC ya sanar mani da cewa an tabbatar kimanin layuka miliyan 6.775.

“Hakan na nufin cewa layuka miliyan 2.242 ne kadai ba a tabbatar ba. Don haka muna so a tabbatar da su kafin ko a ranar 25 ga watan Satumba, 2019”, inji ministan.

Yace bayan wa’adin da aka bayar, NCC tayi aiki akai sannan ta toshe layukan.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamna: Gwamnan PDP ya lallasa dan takarar APC a kotun zabe

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ministan sadarwa na Najeriya, Dr Isa Ali Pantami ya ce a halin da ake ciki yanzu akwai kimanin layukan wayar salula miliyan 9 da ake amfani da su a Najeriya ba tare da rajista ba.

Isa Ali Pantami ya ba wa hukumar kula da ma’aikatun sadarwa ta kasa wato NCC umarnin cewa su gaggauta rufe layukan har sai masu layin sun bayyana kawunansu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel