Shugaba Buhari ya nada Muhammad Sagagi, Charles Soludo da wasu 6 manyan mukamai

Shugaba Buhari ya nada Muhammad Sagagi, Charles Soludo da wasu 6 manyan mukamai

A ranar Litinin, 16 ga Satumba, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wasu mutane takwas cikin majalisar masu bashi shawara kan harkan tattalin arziki.

Legit.ng Hausa ta samu rahoto daga hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, inda ya bayyana cewa wannan sabuwar kwamiti da Buhari ya nada za su rika magana da shi kai tsaye ba tare da wani dan aike ba.

Hakazalika, zasu rika ganawa da shugaba Buhari bayan watanni uku-uku watau sau hudu a shekara.

A cewarsa: "Kwamitin bada shawara kan tattalin arzikin za su rika baiwa shugaban kasa shawara ne kan harkokin tattalin arziki wanda ya kunshi fashin baki kan kudi, habaka tattalin arziki ta hanyar hada kai da wasu ministoci.

Za su rika ganawa da juna sau daya wata tare da ganawa da shugaban kasa sau hudu a shekara. Amma shugaban kwamitin zai iya ganawa da shugaba Buhari a duk lokacin da ya bukata."

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin gwamnan Adamawa da Sanata Elisha Abbo

Wadanda Buhari ya nada sune:

1.Farfesa Doyin Salami – Shugaban

2. Dr. Mohammed Sagagi – mataimakin shugaba

3. Farfesa . Ode Ojowu – Mamba

4. Dr. Shehu Yahaya – Mamba

5. Dr. Iyabo Masha – Mamba

6. Farfesa Chukwuma Soludo – Mamba

7. Mr. Bismark Rewane – Mamba

8. Dr. Mohammed Adaya Salisu – Sakatare

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel