Obasanjo ya bawa Najeriya shawara a kan matakin da ya kamata ta dauka a kan kasar Afrika ta Kudu

Obasanjo ya bawa Najeriya shawara a kan matakin da ya kamata ta dauka a kan kasar Afrika ta Kudu

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya tsoma baki a kan rikicin kai wa bakin haure dake zaune a kasar Afrika ta kudu hari.

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar 'yancin Inkatha, Mangosuthu Buthelezi, ya hsawarci kasashen da ake kai wa jama'arsu hari da su shigar da korafi a hukumar hadin kan kasashen Afrika (AU) tare da daukan wasu matakan idan hakan bai kawo karshen lamarin ba.

Obasanjo ya yi Alla-wadai da duk wata kasar Afrika da ta kasa magance kai wa 'yan Afrika hari a cikin kasar ta.

A ranar Litinin ne kasar Afrika ta Kudu ta tura jakadu na musamman zuwa Najeriya da sauran kasashen Afrika domin jajanta musu da nuna rashin jin dadi a kan hare-haren da aka kai wa 'yan kasashensu a da ke harkokin kasuwanci a kasar Afrika ta Kudu.

Legit.ng ta rawaito cewa shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, ya roki gwamnatin Najeriya ta yi masa afuwa kan hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya dake zaune a kasarsa.

DUBA WANNAN: Dan adawar da aka bawa mukami a gwamnatin Buhari ya yi murabus, ya fadi dalili

Wakilan shugaban kasan na musamman daga kasar Afirka ta kudu sun mika kokon barar hakurin al'ummar kasarsu ga shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Aso Villa Abuja.

Ramaphosa ya aiko wakilai uku na musamman zuwa kasashen Afrika bakwai, wanda ya hada da Najeriya domin neman afuwar kasashen.

Hakan ya biyo bayan ihu da zage-zagen da shugaban kasar Afrika ta kudun, Cyril Ramaphosa, ya sha a kasar Zimbabwe ranar Asabar yayinda ya halarci taron jana'izar tsohon shugaban kasar, Robert Mugabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel