Farfesa Tijjani Bande zai soma aiki a ofis a matsayin Sakataren UNGA

Farfesa Tijjani Bande zai soma aiki a ofis a matsayin Sakataren UNGA

Mun ji cewa babban Wakilin Najeriya a majalisar dinkin Duniya, Tijjani Muhammad Bande, ya shirya kama aiki a kan kujerar da ya samu a babban zauren majalisar dinkin Duniya UNGA.

Farfesa Tijjani Muhammad Bande zai shiga ofis ne a matsayin shugaban zauren UNGA na majalisar dinkin Duniya kamar yadda Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya ya fada.

Garba Shehu ya fitar da wani jawabi a farkon makon nan inda ya bayyana cewa har za a shirya wata liyafa a Hedikwatar majalisar Dinkin Duniyar da ke birnin New York na kasar Amurka.

Za a yi wannan biki ne yau Litinin 16 ga Watan Satumba da kuma gobe Talata watau 17 ga Satumban 2019. Najeriya za ta aika Wakilan ta na musamman domin su halarci wannan biki.

KU KARANTA: Najeriya ta yi damarar yin koyi da kasar Sin wajen bunkasa tattali

Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa wadanda za su halarci wannan taro sun hada shugaban hukumar tsaro na NIA na kasa watau Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da kuma Ministan waje.

Geoffrey Onyeama da kuma Garba Shehu wanda shi ne babban mai taimakawa shugaban kasa wajen harkokin yada labarai za su halarci wannan biki a madadin Najeriya da gwamnatin ta.

An zabi Muhammad- Bande ne a matsayin shugaban zauren na UNGA a farkon watan Yulin bana. Bande zai rike wannan kujera na tsawon shekara guda inda zai yi aiki da shugaban majalisar.

Kokarin ganin dabbaka muradun SDG yana cikin manyan alhakin da ke kan Farfesa Bande da zarar ya dare kan wannan kujera. Haka zalika zai maida hankali kan tsaro da tattalin arziki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel