EFCC ta kama wani ma’aikacin banki kan zargin satar N137m

EFCC ta kama wani ma’aikacin banki kan zargin satar N137m

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) reshen Ibadan ta kama wani mai suna Olumide Agbabiaka ma'aikacin banki kan zargin sace naira miliyan 137.

Hakan na kunshe ne a wani jawabin daga kakakin hukumar, Mista Tony Orilade wanda ya saki a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba a Ibadan.

Ya bayyana cewa kamun Agbabiaka ya biyo bayan karar da jami'in tsaron bankin reshen jihar ya shigar.

Orilade ya bayyana cewa an zargi mai laifin da karkatarwa da kuma sace kudade daga asusun wani kwastama a Ibadan. Yace wanda ake zargin ya aikata laifin ne tsakanin Janairu 2017 da Yuli.

Yace mai laifin, wanda ya kasance jami'in banki da aka hada da kwastaman, yana ta ziyartan harabar wajen da mutumin ke kasuwanci inda yake karban kudi duk sati.

Orilade yace ya kamata mai laifin ya zuba kudaden ne a asusun mutumin da ke bankin.

Yace maimakon zuba kudaden a asusun mutumin sai kawai ya zuba wani bangare na kudin sannan ya karkatar da sauran zuwa ga amfanin kansa

Ya kara da cewa bayan an gano harkokin damfaran da Agbabiaka ke aikatawa sai aka kaddamar da rubutacciyar kara akansa.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamna: Gwamnan PDP ya lallasa dan takarar APC a kotun zabe

Orilade ya bayyaa cewa mai laifin har ila yau ya bada wani bangare daga cikin kudaden da ya sata ga mutane a matsayin bashi

Ya kuma bayyana cewa an kwato wasu daga cikin kayayyakin sannan anyi rijistansu a matsayin shaidu, sannan kuma cewa za a gurfannar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel