Zaben gwamna: Gwamnan PDP ya lallasa dan takarar APC a kotun zabe

Zaben gwamna: Gwamnan PDP ya lallasa dan takarar APC a kotun zabe

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zama a Ibadan a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, ta jaddada nasarar Gwamna Seyi Makinde na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Adebayo Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne ya shigar da kara akan Makinde a zaben gwamna da aka yi a jihar a ranar 9 ga watan Maris.

Kamfani dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Adelabu da jam’iyyarsa ta APC na kalubalantar kaddamar da Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Oyo da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tayi.

Makinde ya samu kuri’u 515,621 wajen kayar da abokin adawarsa, Adelabu wanda ya samu kuri’u 357,982.

Jam’iyyar PDP da hukumar zabe na cikin wadanda ake kara.

Masu karar sun bayyanna cewa Makinde bai samu mafi akasarin kuri’u ta hanyar doka ba, cewa zaben na cike da zarcewar kuri’u da kuma rashin bin dokar zabe.

Adelabu, ya roki kotu da ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya kara da cewa shine ya samu adadin kuri’un da doka ta yarda dashi, don haka kotun zaben ta soke zaben sannan tayi umurnin sake sabon zabe.

Shugaban kotun zaben, Justis Muhammed Sirajo wanda ya yanke hukunci yace shaidar da jami’an rumfar zabe da karamar hukuma da masu kara suka gabatar baa bun dogaro bane.

A cewar kotun zaben, jami’an basu fadi gaskiya ba kawai sun dogara ne akan abunda jami’an rumfunar zabe suka fada masu.

Kotun zaben ta bayyana cewa masu karar sun gaza gabatar da takardun da suka kamata wada zai taimaka mata wajen tabbatar da kirgan kuri’un.

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohin da suke da mutane da suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu

Sirajo wanda ya bayyana cewa karar bai da fa’ida sannan kuma cewa an yi watsi da ita, ya ci tarar masu karar N200,000.

A hira da manema labarai, lauyan masu kara, Mista Akin Oladeji, ya bayyana cewa za su yanke shawara kan mataki na gaba da za su dauka bayan nazarin hukuncin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel