Jerin jihohin da suke da mutane da suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu

Jerin jihohin da suke da mutane da suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu

Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje ta bayyana jihohin da suka fi yawan mutane da suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu.

Tace mutane 187 ne suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu.

A cewar Dabiri, jihar Ogun ce ke da mafi yawan mutane da suka dawo daga kasar. Ta bayyana hakan yayinda take jawabi a taron manema labarai na duniya a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba.

Da take ciki gaba da bayani, ta bayyana cewa an tattara bayanan wadanda suka dawo daidai da jihohinsu, sannan gwamnnin jiharsu ne za su dauki nauyinsu.

Ga jerin jihohin:

Jihar Ogun - 30

Jihar Imo - 28

Jihar Oyo - 23

Jihar Abia - 7

Jihar Anambra - 13

Jihar Delta - 15

Jihar Ebonyi - 2

Jihar Edo - 13

Jihar Ekiti - 6

Jihar Enugu - 7

Jihar Kwara - 3

Jihar Lagos - 7

Jihar Osun - 6

Jihar Ondo - 6

Jihar Kogi - 1

Jihar Benue - 1

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jakadun Afrika ta Kudu sun iso Abuja domin tattauna zaman lafiya da Buhari

Ta kuma ce jerin na dauke da bayanan wadanda suka dawon inda za a mika su ga jihohi daban-daban domin tabbatar da yi musu rijista yadda ya kamata, jaridar The Cable ta ruwaito.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel