Najeriya ta fara samun bunkasar tattalin arziki bayan rufe iyakokin da muka yi - Buhari

Najeriya ta fara samun bunkasar tattalin arziki bayan rufe iyakokin da muka yi - Buhari

Tun gabanin a yi wata tafiya mai nisa, shugaban Muhammadu Buhari ya ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dangane da matakin wucin gadi da gwamnatinsa ta dauka kan rufe iyayakokin kasa na Najeriya.

Muryar Duniya ta ruwaito cewa, furucin shugaban kasa Buhari ya zo ne a yayin karbar bakuncin wata kungiyar 'yan kasuwa, masana'antu da kuma monama a fadar sa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Shugaba Buhari ya ce a halin tun gabanin a je ko ina, Najeriya ta fara samun bunkasar tattalin arziki kan matakin da ta dauka na rufe iyakokin ta na kasa da aka yi, lamarin da ya ce an yanke hukuncin hakan ne domin magance badakalar shigo da kayayyaki na fasakwauri.

A kwanan baya ne dai kungiyar raya tattalin arzikin kasanec Yammacin Afirka ta ECOWAS, ta nemi shugaban kasa Buhari da ya sauya shawarar matakin da gwamnatinsa ta dauka na rufe iyakokin kasar.

A yayin da ta ke jan hankalin shugaban kasa Buhari, kungiyar ECOWAS ta ce matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka zai illata kudirin kasashen Yammacin Afirka na samar da shirin hada-hadar kasuwancin bai daya.

KARANTA KUMA: A daina auren Mata da yawa - Sarkin Anka ya gargadi masu karamin samu

Sai dai shugaban Najeriyar ya ce kungiyar ECOWAS ta sha kuruminta domin kuwa gwamnatinsa na nan a kan bakanta na goyon bayan tsarin kasuwancin bai daya a yankin.

Ana iya tuna cewa, watanni kadan da suka shude, shugaban kasa Buhari ya rattabata hannu kan amincewa da yarjejeniya tabbatar da tsarin kasuwancin bai daya a yankin kasashen Afirka ta Yamma, lamarin da ya ce tilas a gudanar da tsarin bisa tanadin doka.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel