Ta'addanci masu garkuwa kashi 4 da suka girgiza garin Abuja

Ta'addanci masu garkuwa kashi 4 da suka girgiza garin Abuja

Babu shakka ta'addancin masu garkuwa da mutane ya yadu a birnin Abuja cikin watan da ya gabata, inda aka samu rahoton yadda mutane da dama suka tsinci kansu cikin mummunan hali na ni 'ya su.

Ta'addancin masu garkuwa ya sabunta a baya-bayan nan, inda wata matashiya mai shekaru 24, Aisha Umar Ardo, diyar tsohon dan takarar gwamnan jihar Adamawa, Umar Ardo, ta afka tarkon masu garkuwa da misalin karfe 7.45 na Yammacin ranar 14 ga watan Satumba a unguwar Kwame Nkuruma daura da wani kanti na Blinkers Plaza da ke yankin Asokoro.

Mai kula da wannan babban kanti, Emmanuel Ameji, ya labartawa manema labarai yadda 'yan ta'adda suka yi awon gaba da Aisha. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa ta kubuta bayan da aka biya kudin fansa ta kimanin dalar Amurka 15,000.

Wani matashi wanda ya jaddada bukatar a sakaya sunansa bayan ya kubuta daga hannun masu garkuwa, ya bayyana yadda ya shafe tsawon kwanaki uku a hannu masu ta'adar ta neman kudin fansa. Matashin dai ya ce babu kyara ballantana tsangwama yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa tsawon kwanakin da ya shafe tare da wata mata wadda ita ma suka sallame ta rana guda tare da shi.

Ya bayyana yadda wadanda suka yi garkuwa da shi suke babatun yadda al'amura suka tabarbare a kasar nan musamman yadda rashin adalci yayi kane-kane a gwamnati ta yadda babu aikin yi, gami da handama da babakere ta manyan jami'an gwamnati ta zamto al'adar rayuwa ta yau da kullum, lamarin da suka ce ya jefa sauran al'ummar kasar nan cikin kunci.

Iyayen wasu yara biyu da suma suka afka tarkon masu garkuwa da mutane, sun hau kujerar naki ta zayyana wa manema labarai yadda suka kwashe da masu ta'adar, inda mahaifin su bai gushe ba wajen cewa duk wanda bai yadda da rahoton ba ya na fatan zai tsinci kansa cikin irin halin da suka fada.

KARANTA KUMA: Gwamnonin PDP 4 sun kauracewa taron jam'iyyar na reshen Kudu maso Gabas

Haka kuma wata mata Helen Nwakachukwu, ta zayyana yadda masu garkuwa da mutane bayan lakada mata duka tsiya suka kuma yashe dukkanin kudadenta da ke killace a asusun ajiya na banki. Helen dai ta ce sun yi mata ta karfin tsiya da a dole sai da ta bayyana masu lambobin sirri na katin banki wato ATM.

A yayin da kwamishinan 'yan sandan Abuja, Bala Chiroma ya shaidawa manema labarai na jaridar Daily Trust cewa, an jibge jami'an tsaro a duk wani kwararo da sako da ake zargin miyagu za su ribata wajen cin karen su babu babbaka, al'umma da dama na ci gaba da alakanta wannan annoba da mulkin kama karya da kuma gazawar gwamnati wajen fuskantar da akalar jagoranci a bisa turbar da ta dace.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel