Rikicin jam'iyyar PDP ya yi kamari kan zaben gwamnan jihar Kogi

Rikicin jam'iyyar PDP ya yi kamari kan zaben gwamnan jihar Kogi

Tsananin riciki ya kara zurfi tare da rincabewa biyo bayan kammala zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar Kogi na jam'iyyar PDP. Za a gudanar da zaben gwamnan jihar ne a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP a yanzu ya bayu ne biyo bayan nasarar da Musa Wada ya samu a matsayin wanda ya lashe tikitin takara na jam'iyyar bayan da samu tulin kuri'u 748 yayin zaben fidda gwanin takara.

A yayin da rage saura watanni biyu a gudanar da zaben gwamnan a jihar Kogi, Sanatan jihar mai wakilcin shiyyar Yamma, Dino Melaye, da kuma Abubakar Imam, dan tsohon gwamnan jihar Ibrahim Idris, sun hau kujerar naki ta amincewa da sakamakon zaben da jam'iyyar ta fitar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Abubakar ya samu kuri'u 710 a matsayin wanda ya zo a na biyu, yayin da Sanata Dino ya samu kuri'u 70 a zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar Kogi na PDP da aka gudanar cikin birnin Lokoja a ranar 3 ga watan Satumba.

KARANTA KUMA: Gwamnonin PDP 4 sun kauracewa taro jam'iyyar na reshen Kudu maso Gabas

Tuni dai Sanata Melaye da Abubakar suka shigar da korafin su gaban kwamitin amintattu na jam'iyyar tare da cewa ba su amince da sakamakon zaben ba, biyo bayan yadda 'yan bindiga suka tayar da hargitsi gabanin kammalarsa.

Baya ga haka, Abubakar Imam ya garzaya kotu inda yake neman ta tabbatar da shi a matsayin ainihin dan takarar gwamnan PDP na jihar Kogi. Labarin hakan ya zo ne ta harshen mai magana da yawun kungiyar yakin neman zabensa, Shaba Ibrahim, yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba ta makon da ya gabata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel