Buhari zai kammala gyarar wutar Najeriya kafin karshen mulkinsa – Minista

Buhari zai kammala gyarar wutar Najeriya kafin karshen mulkinsa – Minista

Ministan wutar lantarki, Injiniya Mamman Saleh dan mutane Taraba ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tabbatar da ingantaccen wutar lantarki wanda babu daukewa a Najeriya kafin wa’adin mulkinsa ya kare.

Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa Ministan ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da ya kai ziyarar gani da ido zuwa wasu tashoshin wutar lantarki guda biyu dake unguwannin Mando da Kudenda a garin Kaduna.

KU KARANTA: Akwai bukatar ku zage damtse a kan batun wutan lantarki – Sarkin Zazzau ga FG

A jawabinsa, majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan ya bayyana cewa gwamnatinsu zata kammala duk wasu manyan ayyukan wutar lantarki a Najeriya, kuma da zarar an kammala ayyukan, wuta za ta daidaita a Najeriya gaba daya.

Ministan ya kai wannan ziyara ne tare da karamin ministan lantarki, Goddy Agba, inda yace baya ga kara adadin wutar da ake samarwa a Najeriya, tashar wuta ta Kudenda za ta taimaka wajen samar da wuta a Kaduna, Kano da Jos.

Daga karshe, ministan ya bayyana gamsuwar da matakin da aikin tashar wutar ya kai, amma ya gargadi yan kwangilolin dake ayyukan da su gaggauta kammala aikinsu ba tare da bata lokaci ba.

A wani labarin kuma, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ya bukaci gwamnatin tarayya ta tashi tsaye, ta yi da gaske kamar tana yi game da batun samar da dawwamammen wutar lantarki a Najeriya gaba daya.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakoncin ministan wutar lantarki, Injiniya Mamman Saleh da karamin ministan wuta, Goody Jedi-Agba a fadarsa dake birnin Zazzau a ziyarar da suka kai domin kaddamar da wani tashar wutar lantarki da aka yi ma gyara na 2x7.5MVA a cikin jami’ar Ahmadu Bello.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel