Ku yi hakuri - Shugaban kasar Afirka ta kudu ya nemi afuwan yan Najeriya

Ku yi hakuri - Shugaban kasar Afirka ta kudu ya nemi afuwan yan Najeriya

Shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, ya roki gwamnatin Najeriya ta yi masa afuwa kan hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya dake zaune a kasarsa.

Wakilan shugaban kasan na musamman daga kasar Afirka ta kudu sun mika kokon barar hakurin al'ummar kasarsu ga shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Aso Villa Abuja.

Ramaphosa ya aiko wakilai uku na musamman zuwa kasashen Afrika bakwai, wanda ya hada da Najeriya domin neman afuwar kasashen.

Wannan abu ya biyo bayan ihu da zage-zagen da shugaban kasar Afrika ta kudun, Cyril Ramaphosa, ya sha a kasar Zimbabwe ranar Asabar yayinda ya halarci taron jana'izar tsohon shugaban kasar, Robert Mugabe.

Hakazalika, shugaban kasan ya zafa zuwa taron gangamin majalisar dinkin duniya da yayi niyyar zuwa a wannan wata.

A makon da ya gabata, shugaba Buhari ya bada umurnin kwaso yan Najeriyan da ke niyyar dawowa gida daga kasar Afirka ta kudu. Kimanin mutane 200 sun dawo ranar Laraba.

Bayan haka, Buhari ya tura wakili na musamman kasar Afirka ta kudu, shugaban hukumar NIA, Ahmed Rufai, domin gabatarwa shugaban kasan rashin jin dadin gwamnatin Najeriya. Bugu da kari, Buhari ya umurci jakadan Najeriya zuwa Afrika ta kudu ya dawo gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel