Yanzu Yanzu: Jakadun Afrika ta Kudu sun iso Abuja domin tattauna zaman lafiya da Buhari

Yanzu Yanzu: Jakadun Afrika ta Kudu sun iso Abuja domin tattauna zaman lafiya da Buhari

Jakadun da Shugaban kasa Cyril Ramaphosa na kasar Afrika ta Kudu ya aiko Najeriya domin tattauna zaman lafiya tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun iso Abuja.

Jakadun karkashin jagoranncin Bobby Monroe, babban jakadan Afrika ta Kudu a Najeriya, sun iso kasar da rana a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba.

Ganawar da suka yi tare da shugaba Buhari a fadar Aso Rock na daga cikin kokarin Afrika ta Kudu wajen ganin ta sasanta lamura wanda hare-haren da aka kaiwa yan Naeriya a kasarta ya haddasa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jakadun zasu kara jaddada wa Najeriya bukatar kada dankon hadin kai tsakanin kasashen Afrika, tare da tattauna hanyoyin da za a sake tabbatar da zaman lumana a tsakanin kasashen biyu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shugaba Ramaphosa ya tura jakadun uku ida za su fara kai ziyara Najeriya sannan su karasa wasu kasashen Afrika shida. da suka hada da Nijar, Ghana, Senegal, Tanzania, Damokradiyyar Congo da kuma Zambia.

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa da mutane ba su yi wa babban birnin Najeriya zobe ba - Yan sanda

An kuma tattaro cewa za su isar da sakon Shugaba Ramaphosa dangane hare-haren da aka kai wa ‘yan wadannan kasashe da ke zaune a Afrika ta Kudu da kuma lalata musu dukiyoyi da aka yi.

Sannan kuma za su kara jaddada matsayar Afrika Ta Kudu wajen bin doka da oda.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel