Za a ci gaba da rufe iyakar kasar har sai an cimma manufa – Babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro

Za a ci gaba da rufe iyakar kasar har sai an cimma manufa – Babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro

Babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Ritaya Manjo Janar Babagana Monguno, yace iyakokin kasar za su ci gaba da kasance a rufe har sai an cimma manufofin da ke tattare da kulle su.

Monguno a fada ma manema laarai a karshen mako cewa aikin hadin gwiwa na tsaro da ke gudana wanda ya sanya aka rufe iyakokin zai fi kwanaki 28 da aka bayyana da farko sannan kuma zai ci gaba da kasancewa a haka har sai an cimma manufofi.

“Babu rana ko wa’adin da zamu kammala wannan shiri sannan mun fara ganin sakamako masu kyau.

“Wannan shiri na daga cikin kokarin raba kasar da ayyukan miyagu ciki hadda fasa kauri da kuma habbaka tattalin arziki.Ana kuma son tsare rayukan jama’a,” inji Monguno.

Ya kara da cewa lamarin rashin tsaro na kara tabarbarewa sakamakon dammar da masu fasa kauri ke samu ta iyakokin kasar.

KU KARANTA KUMA: Garkuwa da mutane: 'Yan bindiga sun sace diyar dan uwan Atiku a Asokoro

Don haka babban mai ba kasar shawara a fannin tsaro, yayi kira ga hadin kai daga kasashen da ke makwabtaka domin cimma maufar shirin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel