Da duminsa: Dan adawar da aka bawa mukami a gwamnatin Buhari ya yi murabus

Da duminsa: Dan adawar da aka bawa mukami a gwamnatin Buhari ya yi murabus

Seun Onigbinde, daya daga cikin wadanda suka kafa BudgIT; wata cibiyar bin kwakwafin aiyukan gwamnati, ya yi murabus daga mukamin da aka bashi a matsayin mai bayar da shawara na musamman ga ministan kasafi da tsare-tsare, Clem Agba.

Onigbinde ya sanar da yin murabus dinsa ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (Tuwita).

"Biyo bayan cece-kuce da surutan da ake yi tun bayan nada ni a matsayin mai bayar da shawara na musamman ga ministan kasafi da tsare-tsare, ina mai sanar da cewa na yi murabus, na ajiye mukamin," a cewar Onigbinde.

Kazalika, ya yi godiya ga minista Clem Ikanade Agba a kan bashi mukamin tare da bayyana hakan a matsayin babbar girmama wa a gare shi.

"Ina mai matukar godiya ga mai girma minista, Clem Ikanade Agba, bisa yarda da ni da ya nuna, kuma ina godiya ga dukkan wadanda suka taya ni murnar samun mukamin. Ina mai nuna jin dadi a kan irin yardar da dumbin jama'a suka nuna a kai na.

"Babban burina shine ganin ganin Najeriya ta yi amfani da albarkatun da take da su wajen kyautata wa jama'a. Na karbi mukamin ne domin bayar da gudunmawa ta wajen ganin hakan ta tabbata.

"Ina yi wa gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, fatan alheri. Zan cigaba da bayar da gudunmawa ta a matsayina na darekta a cibiyar BudgIT, kuma zan cigaba da amfani da matsayina domin wayar da kan 'yan Najeriya a kan yadda ake kashe kudaden harajinsu a gwamnati," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel