Yansanda sun halaka gungun miyagu masu garkuwa da mutane a jahar Kogi

Yansanda sun halaka gungun miyagu masu garkuwa da mutane a jahar Kogi

Hadakan rundunar jami’an tsaron Najeriya da suka hada da Sojoji da Yansandan Najeriya sun yi rawar gani a yayin wani artabu da suka yi da gungun miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane a jahar Kogi, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

A yayin wannan arangama, rundunar hadakan tare da taimakon mafarauta sun samu nasarar halaka yan bindiga guda uku, tare da jikkata wasu yan bindigan guda biyu, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar Kogi ya tabbatar.

KU KARANTA: Akwai bukatar ku zage damtse a kan batun wutan lantarki – Sarkin Zazzau ga FG

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin, ASP William Aya ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace lamarin ya auku ne a ranar 11 ga watan Satumba bayan yan bindigan su 5 sun yi awon gaba da wasu mutane 6 dake tafiya a kan hanyar Iyamoye cikin karamar hukumar Ijumu.

Daga cikin mutanen da yan bindigan suka sata akwai Cif Ganiyu Popoola, kaninsa, Sule Popoola, dan kaninsu, mace guda daya da mijinta, sai kuma wani mutumi da ba’a bayyana sunansa ba.

Bayan yan bindigan sun kwakkwace kudadensu, suka tasa keyarsu zuwa mafakarsu dake cikin kungurmin daji, amma bayan wasu yan sa’o’i sai suka saki Cif Ganiyu Popoola, dan uwasa Sule da wannan matar, da nufin su tafi su nemo kudin fansan sauran mutane 3 dake hannu.

Kafin nan sun dauki lambobin wayoyinsu, sa’annan suka mika musu wayoyin nasu, Popoola yace sun yi tafiya a kasa na tsawon sa’o’i da dama kafin suka isa bakin hanya, inda suka bulla garin Egbeda-Egga, a nan suka hadu da Yansanda 2, wanda suka shaida musu halin da suke ciki.

Ana cikin haka ne sai wasu Sojoji 5 a karkashin jagorancin wani hafsan Soja mai mukamin Manjo suka tarar dasu, nan da nan shugaban mafarautan Egbeda-Egga ya jagorancesu har mafakar yan bindigan ya samu bayanai daga wajen Popoola.

Isarsu mafakar keda wuya ashe yan bindigan sun hangesu, kawai sai suka bude musu, wuta, daga nan aka fara musayar wuta har sai da aka kashe yan bindiga guda 3, yayin da 2 kuma suka tsere da rauni a jikinsu, haka zalika an gano kudi N57,000 da wayoyin salula a jikinsu.

Tuni dai Sojojin suka jibge gawarwakin miyagun a ofishin Yansandan Najeriya dake Iyara da bindigunsu guda 4.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel