Akwai bukatar ku zage damtse a kan batun wutan lantarki – Sarkin Zazzau ga FG

Akwai bukatar ku zage damtse a kan batun wutan lantarki – Sarkin Zazzau ga FG

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ya bukaci gwamnatin tarayya ta tashi tsaye, ta yi da gaske kamar tana yi game da batun samar da dawwamammen wutar lantarki a Najeriya gaba daya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakoncin ministan wutar lantarki, Injiniya Mamman Saleh da karamin ministan wuta, Goody Jedi-Agba a fadarsa dake birnin Zazzau a karshen makon data gabata.

KU KARANTA: Gobara ta tafka mummunan barna a kasuwar garin Jos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ministocin biyu sun isa Zaria ne domin kaddamar da wani tashar wutar lantarki da aka yi ma gyara na 2x7.5MVA a cikin jami’ar Ahmadu Bello.

“Akwai bukatar gwamnati ta zage damtse wajen samar da dawwamammen wutar lantarki a Najeriya, wannan zai kara karfin tattalin arziki tare da kara martabar kasar, muna sa ran zuwanka wannan mukamin zai kawo karshen matsalar wuta a Najeriya.” Inji Sarki.

Da yake jawabi yayin kaddamar da tashar wutar, Ministan ya bayyana cewa yana fatan gyaran da aka yi ma tashar wutar lantarkin zai inganta wutar lantarkin da ake samu a jami’ar Ahmad Bello.

A wani labarin kuma, yan kasuwa da dama sun gamu da babbar asara bayan tashin wata gobara a kasuwar Katako dake garin Jos na jahar Filato, wanda ta kona shaguna guda 50 a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa matsalar wutar lantarki ce ta yi sanadiyyar tashin gobarar. Shugaban kasuwar, Yusuf Aliyu ya bayyana cewa an tafka asara ta fi ta naira miliyan 50.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel