Gbajabiamila ya isa jihar Katsina domin koyar wa a wata makarantar sakandire (Hotuna)

Gbajabiamila ya isa jihar Katsina domin koyar wa a wata makarantar sakandire (Hotuna)

- Femi Gbajabiamila, shugaban majalisar wakilai, zai koyar da dalibai a wata makarantar sakandiren gwamnati da ke jihar Katsina

- Gbajabiamila ya fara aikin koyar wa na 'sa kai' a mazabarsa, Surelere 1, a jihar Legas a cikin shekarar 2017

- A cewar mai taimaka a bangaren yada labarai, shugaban majalisar zai koyar makarantun sakandire a dukkan sassan Najeriya

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, zai koyar a babbar makarantar sakandiren 'Pilot' da ke kofar Sauri a jihar Katsina.

Gbajabiamila ya fara aikin koyar wa na 'sa kai' a mazabarsa, Surelere 1, a jihar Legas a cikin shekarar 2017, lokacin yana rike da mukamin shugaban masu rinjaye a zauren majalisa.

A cewar Lanre Lasisi, mai taimaka wa Gbajabiamila a bangaren yada labarai, shugaban majalisar zai koyar makarantun sakandire a dukkan sassan Najeriya.

Lasisi ya ce Gbajabiala zai koyar da daliban makarantar sakandiren unguwar Kofar Sauri 'illolin tu'ammali da miyagun kwayoyi, wanda dama darasi ne a cikin manhajar daliban ta wannan sheakarar.

Bayan koyar wa a makarantar sakandiren, Gbajabiamila zai ziyarci wasu mazauna sansanin gudun hijira a sansaninsu da ke jihar Katsina.

Kazalika, shugaban majalisar zai gana da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, da wasu shugabannin jama' da kuma kungiyoyin matasa dabadaban a jihar.

Gbajabiamila ya isa jihar Katsina domin koyar da daliban da kuma ganawa da gwamna Masari da sauran harkokin da zai gudanar a jihar, kamar yadda ya ke a cikin sanarwar da mai taimaka masa a bangaren yada labarai ya fitar.

Gbajabiamila zai koyar a wata makarantar sakandire a Katsina (Hotuna)
Gbajabiamila ya isa Katsina
Asali: Twitter

Gbajabiamila zai koyar a wata makarantar sakandire a Katsina (Hotuna)
Gbajabiamila ya sauka a Katsina
Asali: Twitter

Gbajabiamila zai koyar a wata makarantar sakandire a Katsina (Hotuna)
Gbajabiamila a Katsina
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel