Garkuwa da mutane: 'Yan bindiga sun sace diyar dan uwan Atiku a Asokoro

Garkuwa da mutane: 'Yan bindiga sun sace diyar dan uwan Atiku a Asokoro

Wasu 'yan bindiga da ya zuwa yanzu ba a san ko su waye ba sun sace wata budurwa, A'ishat Umar Ardo, diyar babban dan siyasa a jihar Adamawa, Dakta Umar Ardo.

An sace A'ishat ne da misalin karfe 7:45 na yammacin ranar Asabar a babban shagon sayayya na 'Blinkers' dake unguwar Asokoro a cikin birnin Abuja.

A wani jawabi mai karancin bayanai da ya wallafa, mahifin Ummi; Dakta Ardo, ya tabbatar da sace diyarsa.

"An sace diya ta, A'ishat Umar (Ummi), mai shekaru 24, a babban shagon sayayya na Blinkers da ke lamba 46 a kan titin Nkwame Nkurma a unguwar Asokoro da misalin karfe 7:45 na yammacin jiya (Asabar).

"Sun gudu da ita a cikin wata mota. Har yanzu ba mu ji labarinta ba, har yanzu kuma ba mu samu kira daga gare su ba. Mu na bukatar addu'ar ku. Na gode," kamar yadda ya ke a cikin sakon Ardo, mahaifin ummi.

DUBA WANNAN: Jerin hanyoyi 15 da shugaba Buhari ya amince a gina a kan biliyan N182

Dakta Ardo dan uwa ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Sai dai, a daren ranar Lahadi rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Abuja ta bayyana cewa tuni ta fara farautar wadanda suka sace A'ishat tare da bayyana cewa sun kubutar da wani lakcara, Abubakar Akali, da masu garkuwa da mutane suka sace ranar Asabar.

A jawabin da ta fitar ta bakin kakakinta na birnin tarayya, Abuja, DSP Anjuguri Manzah, rundunar 'yan sandan ta ce akwai tsaro a cikin birnin tarayya tare da bayar da tabbacin cewa za ta cigaba da kare rayuka da dukiyoyin mazauna Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel