Masu garkuwa da mutane ba su yi wa babban birnin Najeriya zobe ba - Yan sanda

Masu garkuwa da mutane ba su yi wa babban birnin Najeriya zobe ba - Yan sanda

Rundunan yan Sanda reshen babban birnin tarayya tace, sabanin jita-jita da ake ta yayatawa a kafofin yada labarai, masu garkuwa da mutane ba su yi wa babban birnin kasar zobe ba.

Wani jawabi daga Anjuguri Manzah, kakakin yan sandan babban birnin tarayya, ya ba jama'a tabbacin cewa birnin kasar na cikin kwanciyar hankali da tsaro, sannan kuma cewa rundunar yan sanda ta inganta dabarunta na yaki da laifuffuka don tabbatar da tsaro ga rayuka da kaddarori jama'a.

Yace ya dace a bayyana ma al’umma cewa rundunar yan sanda tayi nasara wajen kubutar da lakcaran jami'ar Baze wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 8 ga watan Satumba 2019.

Ya kara da cewa, “Reshen har ila yau tana son ta sanar da al’umma cewa ta soma gudanar cikakkiyar bincike cikin lamarin sace lakcaran wanda ya faru a Asokoro a ranar Asabar 14 ga watan Satumba 2019. Rundunan yan Sandan a halin yanzu tana kokarinta don ganin ta kubutar da wanda lamatin ta cika da shi."

KU KARANA KUMA: Yadda za ka tabbatar da matsayin rijistan layinka domin gudun kada NCC ta toshe ka

Ya jaddada jajircewar reshen rundunan wajen kare rayuka da kaddarori da tura matakan tsaro da suka cancanta wajen kawo karshen lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel