Zaben fitar da gwani ya jawo dubannin za su tsere daga PDP a Jihar Kogi

Zaben fitar da gwani ya jawo dubannin za su tsere daga PDP a Jihar Kogi

Alamu na nuna cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ta samu kan ta a rikicin cikin gida bayan zaben da ta yi wajen tsaida ‘dan takarar gwamna a jihar Kogi inda wasu ke neman sauya-sheka a yanzu.

PDP ta samu kan ta cikin matsala ne a jihar Kogi tun bayan da Injiniya Musa Wada ya lashe tikitin takarar gwamna a zaben 2019. Wannan na iya ba gwamnan APC dama ya cigaba da mulki.

Wasu Jiga-jigan PDP sun fara nuna shirin su na komawa APC ko kuma su tsaya a cikin gidan su yi wa jam’iyyar barna domin kowa ya rasa. 'Yan takara da-dama sun fusata da zaben cikin gidan.

Wani babban Jigon PDP a yankin yammacin jihar Kogi ya fadawa ‘yan jarida cewa jam’iyyar ta na cikin hali war haka. Jigon jam’iyyar ya kyankyasa cewa PDP ba za ta kai labari a babban zabe ba.

Wani jagoran PDP ya fito ya koka da yadda aka wulakanta daya daga cikin masu neman kujerar gwamnan Kogi a PDP watau Abu Ibro wanda ‘Da ne waje wani tsohon gwamna kuma kusa a jihar.

KU KARANTA: Tinubu ya fadi abin da ya sa Atiku ya rasa kara a kotun zabe

Wani daga cikin ‘yan takarar ya koka da yadda aka yi watsi da irin su Abubakar Ibrahim Idris saboda wasu na jin haushin Mahaifinsa. A dalilin wannan ya sa su ka fara shirin sauya-sheka.

Daga cikin wadanda su ka nemi mulki a jam’iyyar PDP su ka rasa, akwai wadanda yanzu sun fara yin kus-kus da gwamna Yahaya Bello. Hakan na nufin su na daf da shirin yi wa PDP zagon-kasa.

Akwai ‘dan takarar da yake kukan cewa an yi rashin adalci wajen hanasa tutar gwamna a 2015, sannan kuma aka dauki tikitin da ya dace a ba shi, aka mikawa Dino Melaye a zaben bana.

Sanata Dino Melaye wanda ya bar APC a bara ya kuma samu takara a PDP ya na cikin wadanda su ka nemi tikitin gwamna a zaben da aka yi kuma ya na cikin fusatattun ‘ya ‘yan jamiyyar a yanzu.

Injiniya Wada Musa wanda PDP ta tsaida shi ne zai kara da gwamna mai-ci Yahaya Bello a zaben da za ayi cikin tsakiyar Nuwamban 2019. A bangaren APC ba a samu wani rikici na cikin gida ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel