Allah sarki: Wani mutum ya rasa matarsa da yara 3 a mummunan hatsarin mota a Benue

Allah sarki: Wani mutum ya rasa matarsa da yara 3 a mummunan hatsarin mota a Benue

Kwanan nan ne wani ibtila’i ya afka ma wani dan Najeriya inda ya rasa iyalinsa baki daya da suka hada da matarsa da yaransa uku a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Akwanga, Nasarawa.

Babu shakka hanyoyin Najeriya na hallaka rayukan mutane da dama fiye da kowani irin hatsarin abun hawa sannan hakan ce ta kasance ga wanan mutumi da aka ambaci sunansa a matsayin Tavershima Jebe.

Ya rasa matarsa da yaransa guda uku yan kwanaki da suka shude a wani hatsarin hanya da ya afku a Akwanga, da ke jihar Nasarawa.

Ukan Kurugh, wani mai amfani da shafin Facebook, ya buga labarin a shafinsa: “Mista Tavershima Jebe ya rasa matarsa da wadanan kyawawan yaran nasa guda uku a wannan mummunan hatsari mota da ya afku jiya sannan ga Tavershima, duniyar ta riga ta zo karshe.”

KU KARANTA KUMA: Yadda za ka tabbatar da matsayin rijistan layinka domin gudun kada NCC ta toshe ka

Allah sarki: Wani mutum ya rasa matarsa da yara 3 a mummunan hatsarin mota a Benue
Allah sarki: Wani mutum ya rasa matarsa da yara 3 a mummunan hatsarin mota a Benue
Asali: Facebook

A wani lamari makamanci haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa mutane 13 sun rasa ransu sakamakon hadarin mota da ya afku a kusa da Unguwan Ciyawa da ke karamar hukumar Eggon na jihar Nasarawa a jiya Lahadi, 15 ga watan Satumba.

Kwamandan hukumar kula da hana afkuwar hadarurruka a jihar, Ismaila Kugu, ya bayyana cewa wadanda abun ya cika da su sun kasance manya 10 da kananan yara uku, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa wasu mutane 11 sun jikkata a hadarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel