Kotu ta aika sammaci ga Okorocha akan zargin take doka

Kotu ta aika sammaci ga Okorocha akan zargin take doka

Wata kotun Majistare a Owerri, jihar Imo ta aika sammaci ga tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, bisa zargin furta kalaman kiyayya.

Gwamnan zai bayyana a kotu a ranar 8 ga watan Oktoba na wannan shekaran.

Gwamnatin jihar Imo ta yi karan Okorocha a gaban kotun bisa zargin cewa tsohon gwamnan na ingiza magoya bayan shi wajen bijirewa gwamnatin.

A karan mai dauke da lamba OW/MISC.79/2019 wanda aka shigar a kotun Majistare a yankin Owerri, Babban Lauyan jihar Imo a madadin gwamnatin jihar ya yi zargin cewa Okorocha ya kasance da dabi’ar yin kalamai dake iya ingiza magoya bayansa akan gwamnati ta hanyar yin amfani da gidan radiyonsa (Reach FM).

Babban Lauyan har ila yau yayi zargin cewa Okorocha, duk da cewa ya kasance zababben sanata, yana shafe lokutansa a Owerri, tare da yin amfani da yan bangan siyasa wadanda aka fi sani da suna ‘Ohaji Boys’ wadanda ya dauka don tayar da zaune tsaye.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Majalisa sun gargadi Minista da Hukumomin Gwamnati kan kashe kudi ba tare da bin doka ba

Gwamnatin jihar har ila yau tayi zargin cewa wani hadimin Gwamna Emeka Ihedioha ya sha duka yayin da yake kan gudanar da aikin tsare-tsaren kotu akan lamarin da ya shafi gidan Okorocha.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel