'Yan Majalisa sun gargadi Minista da Hukumomin Gwamnati kan kashe kudi ba tare da bin doka ba

'Yan Majalisa sun gargadi Minista da Hukumomin Gwamnati kan kashe kudi ba tare da bin doka ba

- 'Yan Majalisa sun gargadi Ministar kudi da Hukumomin Gwamnati kan kashe kudi ba tare da bin doka ba

- Shugabannin kwamitin kudi na majalisar tarayyar, Sanata Solomon Adeola (majalisar dattawa) da James Faleke (majalisar wakilai) ne suka bayar da gargadin

- Sun ce zamani karkatar da kudin shiga ba tare da izini ba da shugabannin hukumomin gwamnati ke yi ya shude, saboda majalisar dokokin tarayya ta tara za ta tabbatar da cewar gwamnatin tarayya ta samu isasshen kudade

Majalisar dokokin tarayya ta gargadi ministar kudi, Zainab Ahmed, da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da ke tattara kudaden shiga akan kashe kudade ba tare da amincewar yan majalisar dokokin tarayya ba kamar yadda doka ta tanadar.

Shugabannin kwamitin kudi na majalisar tarayyar, Sanata Solomon Adeola (majalisar dattawa) da James Faleke (majalisar wakilai), sun bayar da gargadin ne a ranar Asabar bayan wani taron hadin gwiwa da aka gudanar a Lagas.

A wani jawabi daga hadimin Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan kudi, Cif Kayode Odunaro, a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba, yayi bayanin cewa Adeola da Faleke sun gargadi ministar da shugabannin hukumomi gwamnati da su guji aikata irin haka ko kuma su fuskanci fushin majalisar dokokin taraya.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC da magoya bayansa sama da 1000

Adeola, a cewar jawabin, yace zamani karkatar da kudin shiga ba tare da izini ba da shugabannin hukumomin gwamnati ke yi ya shude, saboda majalisar dokokin tarayya ta tara za ta tabbatar da cewar gwamnatin tarayya ta samu isasshen kudaden shiga domin aiwatar da manufofi ga mutane da kuma shirye-shiryen ci gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel