An cafke wani Bawan Allah da laifin sukar ‘Yan Sanda a Kano

An cafke wani Bawan Allah da laifin sukar ‘Yan Sanda a Kano

Bashir Galadanci, wani ‘dan gwagwarmaya a Kano ya shiga hannun Dakarun SARS masu maganin fashi da makami. Mun samu wannan labari ne daga jaridar nan ta Daily Nigerian jiya.

A Ranar 15 ga Watan Satumba, 2019, mu ka ji cewa Dakarun SARS sun cafke Mista Bashir Galadanci a dalilin caccakar Kakakin jami’an ‘yan sandan Kano, Abdullahi Haruna da yake yi.

Galadanci ya na fitowa shafinsa na Facebook ne ya na yawan sukar Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan na jihar tun da aka turo shi aiki a Kano. Wannan ya sa yake tsare tun makon jiya.

DSP Haruna ya bayyana cewa ba sukar shi da Galadanci yake yawan yi ne ainihin abin da ya sa aka yi ram da shi ba. Asali ma babban jami’in ‘yan sandan ya nuna bai da cikakken labarin abin.

“Ba ni ma da labarin cewa an kama wani mai wannan suna, har sai da na tambayi jami’in da ke kula da SARS.”

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace Malamin jami'a da wasu Bayin Allah

“Ba a kama sa don yana sukar karai kai-na ba; sai dai saboda shiga cikin sha’anin ‘yan sanda ba tare da izni ba.”

DSP Haruna yake cewa wannan danyan aiki da Galadanci yake yi, ya jefa kaf jami’an ‘yan sanda cikin wani hali. Yanzu dai yana tsare a hannun jami’an na SARS na tsawon akalla kwanaki uku.

“Mun yi amanna cewa akwai wasu ‘yan cikin-gida ne da su ke ba shi bayanai na sirri, kuma da aka tasa shi, ya soma fallasa wannan game da wadanda ke ba shi labarai a cikin mu.” Inji Haruna

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel