Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC da magoya bayansa sama da 1000

Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC da magoya bayansa sama da 1000

Sama da mambobin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) 1000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Sapele da ke jihar Delta.

Masu sauya shekar wadanda suka samu tarba a APC a karshen mako a sakatariyar APC da ke karamar hukumar Sapele, sun samu jagorancin wani tsohon kwamishinan jihar, Abraham Bobo.

Sauran manyan jiga-jigan PDP da suka sauya sheka daga jam’iyyar sune Cif W. Ayomanir, Onoriode Temiagi, Dr. Joseph Ogodo, Mista Anthony Ayomanor, Sunday Umukoro da kuma Cif Onomor tare da magoya bayansu.

Sai dai kuma, jaridar Sun ta ruwaito cewa sauya shekarsu na da nasaba da rikicin cikin gida da ya billo a PDP reshen Sapele, kan wasu nade-naden mukaman siyasa da Gwamna Ifeanyi Okowa da shugabancin PDP a jihar suka yi.

KU KARANTA KUMA: Masu yi mani izgili a kafafen sada zumunta su na bani dariya – Inji Yemi Osinbajo

Da yake tarban masu sauya shekar a madadin Shugaban APC a jihar, Jones Erue, mataimakin Shugaban jam’iyyar, Injiniya Elvis Ayomanor ya bayyana cewa jam’iyyar za ta kare gidan gwamnatin jihar, Asaba, cewa jam’iyyar ce za ta yanta mutanen jihar Delta daga rashin kokarin gwamnatin PDP.

Ayomanor yace duba ga manyan mutanen da ke jam’iyyar, APC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen zama jam’iyya mai mulki a jihar nan ba da jimawa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel