An yi ba-ta-kashi tsakanin Sojoji da Boko Haram a kusa da Jami’ar Borno

An yi ba-ta-kashi tsakanin Sojoji da Boko Haram a kusa da Jami’ar Borno

An shiga cikin wani hali na la-hau-la a daren jiya Lahadi, 15 ga Watan Satumba, 2019, inda ‘yan ta’addan Boko Haram su ka nemi su kai hari a babban jami’ar tarayya da ke Maiduguri a Borno.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, Sojoji sun yi namijin kokari wajen hana ‘yan ta’adda kai faramaki a jami’ar Maiduguri wanda aka fi sani da UNIMAID yayin da ake shirin gama zango.

Wadanda su ke kusa da makarantar sun tabbatar da cewa an ta ji barin bindiga daga yankin titin Maiduguri zuwa Bama. A daidai wannan bangare ne dakin kwanan ‘dalibai mata na jami’ar yake.

An dauki fiye da sa’a guda ana jin ruwan bindigogi a wannan wuri cikin daren. Wani babban jami’in soja ya tabbatar da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram ne su ka nemi su kai hari a Maiduguri.

Jami’in sojan ya bayyana cewa Dakarun Sojin kasar sun takawa ‘yan ta’addan burki. Daga bisani wannan hari ya tsorata ‘yan makarantar inda wasu su ka nemi su tsere domin su tsira da ransu.

KU KARANTA: An yi wata gobara a kasuwar Jos da ke Jigar Filato

Jami’an tsaron da ke cikin Jami’ar ne su ka hana yaran barin makarantar. Wasu Sojoji da su ka yi magana da ‘yan jarida a boye su ka bayyana wannan. A karshe dai komai ya lafa ya dawo daidai.

Wata ‘Daliba da ke dakin mata da ake kira BOT ta bayyana halin da su ka shiga inda ta ce duk sun koma su na jiran ikon Allah. A halin yanzu ‘yan makarantar su na jarrabawar zango na biyu ne.

Haka zalika wata ‘Daliba da ke dakin kwana na Aisha Buhari ta shaidawa 'yan jarida cewa duk sun ji karar bindiga inda kowa ya kwanta yana salati. A karshen abin ya lafa wajen karfe 11:00.

Sojojin Amurka sun hallaka Yaron Osama Bin Laden a wani hari da su ka kai wa Al-Qaeeda. Shugaba Donald Trump ya fito ya ce lallai sun kashe Hamza Bin Laden wani 'Dan gidan Osama.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel