Gobara ta tafka mummunan barna a kasuwar garin Jos

Gobara ta tafka mummunan barna a kasuwar garin Jos

Yan kasuwa da dama sun gamu da babbar asara bayan tashin wata gobara a kasuwar Katako dake garin Jos na jahar Filato, wanda ta kona shaguna guda 50 a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito shaidun gani da ido sun bayyana cewa matsalar wutar lantarki ce ta yi sanadiyyar tashin gobarar. Shugaban kasuwar, Yusuf Aliyu ya bayyana cewa an tafka asara ta fi ta naira miliyan 50.

KU KARANTA: Ya yi marisa: Dansanda ya Sassari mutane 9 bayan ya yi tatil da barasa a gidan rawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kasuwar, Malam Aliyu ya bayyana cewa shaguna guda 36 ne suka kone kurmus, yayin da wasu shaguna 14 suka kone rabi da rabi.

Aliyu ya kara da cewa sun nemi hukumar wutar lantarki ta Jos, JEDC, dasu dinga kashe wutar kasuwar idan dare ya yi domin gudun aukuwar gobara, sa’annan ya nemi gwamnati ta taimaka musu wajen samun kudin da za’a sanya na’urar kashe wutar.

A wani labari kuma, gungun miyagu yan bindiga sun kai wata mummunan farmaki a kauyen Katsira Tsauna dake cikin karamar hukumar Sabon Birni inda suka halaka wasu matasa guda uku ba laifi fari ba laifin baki.

Miyagun sun kai harin ne da yammacin Asabar, 14 ga watan Satumba a kan babura guda 5 goyon bibbiyu, inda baya ga kashe matasan, sun kuma jikkata wasu mata guda uku, wanda a yanzu haka suna samun kulawa a babban asibitin garin Sabon Birni.

Wani mazaunina garin yace: “Sun kashe samari guda 3, sa’annan suka jikkata mata 3, da ba don jami’an tsaro sun farga da wuri ba da adadin wadanda zasu kashe ya haura.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel