Gungun miyagu sun kashe mutane 6 a wani hari da suka kai jahar Sakkwato

Gungun miyagu sun kashe mutane 6 a wani hari da suka kai jahar Sakkwato

Gungun miyagu yan bindiga sun kai wata mummunan farmaki a kauyen Katsira Tsauna dake cikin karamar hukumar Sabon Birni inda suka halaka wasu matasa guda uku ba laifi fari ba laifin baki, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito miyagun sun kai harin ne da yammacin Asabar, 14 ga watan Satumba a kan babura guda 5 goyon bibbiyu, inda baya ga kashe matasan, sun kuma jikkata wasu mata guda uku, wanda a yanzu haka suna samun kulawa a babban asibitin garin Sabon Birni.

KU KARANTA: Wani Musulmi ya fille kansa saboda tsananin alhinin shiga sabuwar shekarar Musulunci

Wani mazaunina garin yace: “Sun kashe samari guda 3, sa’annan suka jikkata mata 3, da ba don jami’an tsaro sun farga da wuri ba da adadin wadanda zasu kashe ya haura.”

Haka zalika a wani makamancin wannan da yan bindiga suka kai a kauyen Gardin Ginge, sun kashe mutane 3, sa’annan suka yi awon gaba da shanu da awakai da dama.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Sakkwato, Muhamamd Sadik ya tabbatar da hare haren. Wadannan hare hare suna faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jahar Zamfara ta yi sulhu da yan bindiga, amma kuma sai hare haren suka karu a jahar Sakkwato.

A yanzu haka dai ita ma gwamnatin jahar Sakkwato ta fara kokarin shiga tattaunawar sulhu da yan bindigan kamar yadda rahotanni suka tabbatar, kuma kwamishinan tsaro na jahar, Garba Moyi ne yake jagorantar kokarin tattaunawar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel