Ya yi marisa: Dansanda ya sassari mutane 9 bayan ya yi tatil da barasa a gidan rawa

Ya yi marisa: Dansanda ya sassari mutane 9 bayan ya yi tatil da barasa a gidan rawa

Akalla mutane 9 ne suka samu munanan rauni sakamakon sara da suka da suka samu daga wajen wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya daya debi barasa son ransa, ya sha ya yi mankas abinsa!

Jaridar Punch ta ruwaito wannan Dansanda mai suna Taiwo Orisadare ya aikata haka ne a daren Juma’a a wani gidan rawa dake garin Akuren jahar Ondo, kuma dansandan yana aiki ne a ofishin Area Commander.

KU KARANTA: Wani Musulmi ya fille kansa saboda tsananin alhinin shiga sabuwar shekarar Musulunci

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa rikicin ya samu asali ne a lokacin da Dansandan ya fara cin zarafin mutanen da suka shiga gidan rawan, kuma a lokacin yana cikin halin maye.

“Ya fara marisa ne a lokacin, kuma baya saurara ma kowa a gidan rawar, daga nan ne kawai sai ya zaro wuka yana sarar mutanen da ita, ya yanki wannan ya soka ma wannan a haka ya illata mutane 9, da kyar aka ci karfinsa.” Inji shaidan.

Shi ma wani da lamarin ya auku a gabansa kuma ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an garzaya da mutane zuwa asibitoci daban daban dake garin Akure, sai dai yayin da wasu suke warwarewa, wasu kuma suna cikin mawuyacin hali a dalilin saran.

Da aka tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar, Femi Joseph don jin ta bakinsa, shi ma ya tabbatar da aukuwar rikicin, kuma yace shi kanshi Dansandan ya samu rauni, kuma yana samun kulawa a asibiti.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel