An sace lakcara, matasa biyu da wasu mutane 5 a kwaryar birnin Abuja

An sace lakcara, matasa biyu da wasu mutane 5 a kwaryar birnin Abuja

Batun sace mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa ba sabon abu bane yanzu a sassan Najeriya, sai dai lamarin ya dauki sabon salo bayan an samu rahoton sace mutane a kalla biyar a cikin sa'a 24 a cikin kwaryar birnin Abuja.

Wata majiyar jami'an tsaro ta shaida wa jaridar 'The Cable' cewa daga cikin mutanen da aka sace akwai; Abubakar Alkali; malami a jami'ar Base dake Abuja da wasu matasa biyu da aka sace a hanyarsu ta dawowa daga wurin lakcar Alqur'ani mai girma a unguwar Wuse 'Zone 6', an sace su ne ranar Asabar.

Anjuguri Manzah, kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, ya tabbatar wa da jaridar faruwar lamarin, amma bai yi karin bayani ba.

Daga cikin mutanen da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka sace su akwai wata mai suna Hannah Azuibuike, wacce aka sace a daura da Habiba 'Plaza' dake unguwar Maitama da misalin karfe 8:30 na dare, da Ummi Ardo, wacce aka sace a wajen wani shagon sayayya da ke unguwar Asokoro.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda masu nasaba da IS sun kashe sojojin Najeriya 9, 27 sun bata

A wani jawabi mai karancin bayanai da ya wallafa, mahifin Ummi; wani dan siyasa a jihar Adamawa, ya tabbatar da sace diyarsa.

"An sace diya ta, A'ishat Umar (Ummi), mai shekaru 24, a babban shagon sayayya na Blinkers da ke lamba 46 a kan titin Nkwame Nkurma a unguwar Asokoro da misalin karfe 7:45 na yammacin jiya.

"Sun gudu da ita a cikin wata mota. Har yanzu ba mu ji labarinta ba, har yanzu kuma ba mu samu kira daga gare su ba. Mu na bukatar addu'ar ku. Na gode," kamar yadda ya ke a cikin sakon Ardo, mahaifin ummi.

The Cable ta ce bata samu damar tattauna wa da 'yan uwan wadanda aka sace ba, amma Manzah ya ce rundunar 'yan sanda zata fitar da jawabi a kan faruwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel