Jerin hanyoyi 15 da shugaba Buhari ya amince a gina a kan biliyan N182

Jerin hanyoyi 15 da shugaba Buhari ya amince a gina a kan biliyan N182

A yayin taron majalisar zartar wa ta kasa (FEC) da aka yi ranar Laraba, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bayar da kwangilar gina sabbin hanyoyi da kuma gyaran wasu tsofi a kan kudi biliyan N182bn, a cewar fadar shugaban kasa.

A wata sanarwa da Buhari Sallau, hadimin shugaba Buhari, ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce shugaba Buhari ya amince da aikin gina hanyoyi kamar haka:

1. Gina babbar hanyar Lagos zuwa Badagry, sannan ta wuce zuwa Benin Republic. Aikin zai lashe N15,297,762,234.22

2. Gina wasu gadoji guda biyu a kan titin Kontagora zuwa Rijau, wanda za a yi a kan biliyan N1.12

3. Fadada hanyar Kano zuwa Katsina a kan biliyan N9.4

4. Gina hanyar Kontagora zuwa Bangi a jihar Neja, wanda za a yi a kan biliyan N20.3

5. Gyaran gadar Marina zuwa Bonny da gadar Eko, wanda za a yi a kan biliyan N9.2

6. Gyaran hanyar Ibori zuwa Idomi da ke jihar Edo, wanda za a yi a kan kudi N4.5

7. Gina hanyar Ilogu zuwa Ireni a jihar Kwara da Osun, a kan kudi biliyan N18.41

8. Gina gadar Wudil da ke kan titin Kano zuwa Maiduguri, a kan kudi biliyan N2.5

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Yobe ta karbe wani filinta mai girman hekta 3.5 daga hannun rundunar soji

9. Gyaran titin Wukari zuwa Ibi a jihar Taraba, a an kudi biliyan N12.3

10. Gina tashar ruwa da ke Baro a jihar Neja, a kan kudi biliyan N10.6

11.Gyaran titin da ya tashi daga Ajingi, jihar Kano, zuwa Kafin Hausa, jihar Jigawa, a kan kudi biliyan N25

12. Gyaran hanyar Aba zuwa Owerri, a kan kudi biliyan N6.98

13. Gyaran hanyar Kaliyari zuwa Damaturu a jihar Yobe, a kan kudi biliyan N16.9

14. Gina hanyar Yaba zuwa Yangoji a birnin Tarayya, Abuja, a kan kudi biliyan N17.3

15. Gyaran wasu bangarori biyu na hanyar Nnewi zuwa Okigwe a jihar Imo da Anambra, wanda za a yi a kan kudi biliyan N12.7

Tushen labari: Shafin 'Instagram' na Buhari Sallau (Hadimin shugaban kasa)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel