Tsoron mutuwa ya sa mutane sun raunata yayin harbe-harben sojoji a birnin Kano

Tsoron mutuwa ya sa mutane sun raunata yayin harbe-harben sojoji a birnin Kano

Tsautsayi da ba ya wuce ranarsa ya sanya dalibai da dama da kuma mazaunan birnin Kano Dabo sun jikkata, a yayin da wani ayari na rundunar dakarun sojin kasa suka yi harbe-harben harsashi cikin iska a kan hanyoyin Kabuga, Tal'udu da kuma Gadon Kaya.

Jaridar Kano Today wadda ta sauya suna zuwa Kano Focus ta ruwaito cewa, tawagar sojoji cikin ayari na fiye da motoci goma cikin wake da harbe-harben harsashin bindiga cikin iska, ta ribaci wasu manyan hanyoyin Kano da misalin karfe 2.00 na ranar Asabar da ta gabata.

Babu shakka wannan lamari ya jefa daliban kwalejin ilimi ta FCE Kano cikin firgici gami da razani wadda ke Kofar Famfo daura da titin Kabuga. Hakazalika mazauna yankin musamman 'yan kasuwa da matafiya sun nemi mafaka babu shiri.

Da yawa daga cikin wadanda suka tsinci kansu cikin razani sun jikkata tare da salwantar dukiyoyinsu musamman wayoyin salula da alabe ta ajiyar kudi.

KARANTA KUMA: SON ta rufe kamfanonin man-juye 10 a jihar Kano

Wani mashaidin wannan lamari da ya kasance dalibin kwalejin FCE, Nasiru Muhammad, ya ce sautin harbe-harben sojoji ya haddasa masu dimuwa da gudun kar ta kwana wadda ta sanya dalibai da dama suka arce daga dakin jarrabawa rike da takardansu.

Haka kuma wata daliba, Zainab Hassan Ibrahim, wadda ta samu munanan raunuka, ta ce ba za ta iya bayyana yadda lamarin ya kasance ba domin kuwa cikin tsananin firgici ta shallake wata katanga a kwalejin ba tare da farga ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel