Ka daina sukar takwarorin jam'iyyar ka - Gwamnonin PDP sun gargadi Wike

Ka daina sukar takwarorin jam'iyyar ka - Gwamnonin PDP sun gargadi Wike

Gwamnonin babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta PDP, sun gargadi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da ya kiyaye lafuzansa tare da kauracewa sukar takwarorin jam'iyyarsa.

A yayin da gwamnonin ke neman gwamna Wike da ya kame bakinsa wajen suka da caccakarsu, sun nemi da ya basu hadin kai wajen kwatar mulkin kasar daga hannun jam'iyya mai ci ta APC kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan kira na gwamnonin jam'iyyar PDP na zuwa ne yayin da suka gana da gwamna Wike a ranar Juma'ar da ta gabata cikin birnin Fatakwal na jihar Ribas, inda suka jaddada tsayuwar dakan su a akan wannan lamari.

Tawagar gwamnonin bisa jagorancin gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ta hadar da na jihar Umaru Fintiri na jihar Adamawa, Emeka Ihedioha na jihar Imo, Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benuwe da kuma Muhammad Bello Mutawalle na jihar Zamfara.

Bincike manema labarai ya tabbatar da cewa, gwamna Tambuwal ya kasance jagoran wannan tawaga a sanadiyar kusancin sa da gwamnan na jihar Ribas.

A baya bayan nan ne gwamnan Wike ya haddasa wani rudani a jam'iyyar PDP, a yayin da ya fito fili ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara a kotun sauraron karar zabe, lamarin da ya ce wasu takwarorinsa sun aiwatar da hakan ne a bayan fage.

KARANTA KUMA: Tabbas Buhari ya fi Atiku cancantar jagorancin Najeriya - APC reshen Arewa maso Gabas

Ana iya tuna cewa, makonni kadan da suka gabata ne kotun sauraron karar zaben shugaban kasa, ta tabbatar da nasarar shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe babban zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata.

Kotun dai ta yi watsi da korafin dan takarar shugabancin kasar nan na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shigar, bayan da ya kalubalanci sakamakon zaben da cewa bai tsarkaka da gaskiya ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel