SON ta rufe kamfanonin man-juye 10 a jihar Kano

SON ta rufe kamfanonin man-juye 10 a jihar Kano

Hukuma kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya SON, ta rufe wasu kamfanoni 10 na man-juye wato bakin mai a jihar Kano da laifin sayar da gurbataccen kaya ga al'umma.

Shugaban hukumar SON reshen jihar Kano, Alhaji Yunusa B. Muhammad, shi ne ya shaida wa manema labarai wannan rahoto dangane da hukuncin da suka dauka gwargwadon iko da ya rataya a wuyansu.

Alhaji Yunusa ya ce hukumar SON ba za ta rangwanta wa duk wani kamfanin sayar da man juye ba da ta kama da laifin sayar da kayayyaki masu nakasun inganci.

A yayin tauna aya domin tsakuwa ta ji tsoro da cewar wannan lamari na daukar mataki zai ci gaba da gudana, babban jami'in na hukumar SON ya gargadi dukkanin masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci da su tabbatar da ingancin kayayyaki wajen siye da sayarwa.

KARANTA KUMA: Tabbas Buhari ya fi Atiku cancantar jagorancin Najeriya - APC reshen Arewa maso Gabas

A cewarsa, babu sani ballantana sabo a yayin da hukumar SON ta daura damarar bankado miyagun mutane tare da daukar tsauraran hukunce-hukunce a kan masu yin algus wajen sayar da kayayyaki masu nakasun inganci.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwar man-juye na jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi, yayin zantawa da manema labarai na jaridar The Nation ya ce, kungiyar su a kullum tana cikin shirin kiyaye doka tare da bin umarnin gwamnati sau da kafa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel