Masu yi mani izgili a kafafen sada zumunta su na bani dariya – Inji Yemi Osinbajo

Masu yi mani izgili a kafafen sada zumunta su na bani dariya – Inji Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ya gano wasu ‘yan Najeriya su na masa ganin cewa da zarar ya hadu da shugaban kasa Buhari su na magana, to wani sharri ake yi.

Yemi Osinbajo yake cewa a ko yaushe ya dauki hoto tare da shugaban kasa, sai wasu su rikida hoton a rika yi masa izgili. Osinbajo yake cewa irin hakan da mutane ke yi, yana ba shi dariya.

Har ila yau mataimakin shugaban na Najeriya ya na ganin masu yi masa wannan tsiya, su na da hikima matuka. Osinbajo ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro kamar yadda bidiyo ya nuna.

Wasu kan dauki hoton Osinbajo da Mai gidan sa a sanya masu rubutu na maganganun bogi domin raha. Mataimakin shugaban kasar ya kawo misalan irin wannan abu da aka saba masa.

“Duk wani hoto na da Buhari, sai an maida shi kamar ina fadawa shugaban kasar wani mugun kulli ne.”

Osinbajo ya kara da: “Na yarda da damar kowa ya fadi abin da ya ga dama ko da shirmen banza ne.”

KU KARANTA: Kanu zai ja zuga har gaban Majalisar dinkin Duniya

Sai dai Farfesan yace jama’a ba su maida hankali game da abin da ya dace na gaskiya sai sokiburutsu inda har ya kafa misali da zancen satifiket din shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce: “Sai ka dauka ‘yan jarida za su yi bincike domin gano gaskiya game da satifiket din Buhari.” A karshe dai kotu ce ta raba gardama inda ta ce shugaba Buhari ya cancanci tsayawa takara.

“Wata tsohuwar Goggo na ta kira ni a Watan Fubrairu daf da zabe ta na tambaya na meyasa na ajiye aiki. Na fada mata cewa ban yi murabus ba, amma ta kafe cewa ta samu labari a WhatsApp.”

Osinbajo ya bada wannan labari ne domin nuna karfin kafafen yada labarai musamman na zamani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel