Biafra: Nnamdi Kanu zai jagoranci wata tawagar wakilai zuwa majalisar dinkin duniya

Biafra: Nnamdi Kanu zai jagoranci wata tawagar wakilai zuwa majalisar dinkin duniya

Shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutikar kafa kasar 'yan kabilar Igbo, Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, zai jagoranci wata tawagar wakilai zuwa ofishin majalisar dinkin duniya (UN) da ke birnin Geneva a kasar Switzerland.

Da yake sanar da hakan a ranar Lahadi, sakataren yada labaran kungiyar IPOB, Emma Powerful, ya ce ba zasu bayar da bayanai ga jama'a a kan dalilin ziyarar ba.

Jawabin ya ce, "a cigaba da tuntubar shugabannin duniya da shugaban kungiyar IPOB, Mazi Nnamdu Kanu, ke yi domin ganin an kafa kasar Biafra, muna masu farin cikin sanar da mambobin kungiyar Biafra da masoyanta cewa shugaban mu zai jagoranci wata tawagar wakilai zuwa ofishin majalisar dinkin duniya (UN) da ke Geneva, Switzerland, a ranar 18 ga watan Satumba, 2019.

"Ba zamu sanar da dalilin ziyarar ba saboda mun san irin abubuwan da shugabannin Najeriya zasu iya yi domin bata shirin da muke da shi."

DUBA WANNAN: Takardun shaidar kammala karatu: Gwamnan APC zai kori ma'aikata 422 a jiharsa

Kungiyar IPOB ta bukaci 'yan Biafra da ke zaune a kasar Switzerland da sauran kasashen turai da su fito domin tarbar Kanu da tawagarsa tare da bashi goyon baya domin ganin sun cimma burinsu na kafa kasar Biafra.

"Lokacin da shugabanmu ya ziyarci zauren majalisar Turai (EU), ya bayyana cewa ziyara ta gaba da zai kai ita ce zuwa majalisar dinkin duniya sannan daga bisani zai ziyarci fadar mulkin kasar Amurka da ke birnin Washington DC. Yanzu an kammala dukkan shirye-shirye a kan ziyarar da zai kai zuwa majalisar dinkin duniya a cikin sati mai zuwa," Kamar yadda ya ke a cikin sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa kungiyar IPOB za ta cigaba da fafutikar tabbatar da hakkin 'yan Biafra da sauran kananan kabilun Najeriya da ke neman hakkinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel