Kasar Afirka Ta Kudu za ta turo wakilai na musamman Najeriya

Kasar Afirka Ta Kudu za ta turo wakilai na musamman Najeriya

- Shugaban kasar Afirka Ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya gama shirin turo wakilai na musamman Najeriya

- Wakilan ba Kasar Najeriya kadai za su tsaya ba, kasashen da zasu sun hada da kasashen Niger, Ghana, Tanzania, Jamhuriyar Congo da Zambia

- Wakilan na musamman zasu mika sako daga shugaban Ramaphosa ne dangane da rikicin da ya barke a wasu sassan kasar

Shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, ya shirya tsaf don tura wakilai na musamman ga shuwagabannin nahiyar Afirka wadanda suka hada da Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari akan hari da 'yan kasarsa suke kaiwa 'yan wasu kasashen.

Kamar yadda News24 ta sanar, wakilan na musamman zasu isar da sakonni ne ga shuwagabannin kasashe da gwamnatocin kasashen Nahiyar Afirka akan tashin hankali da hargitsi da aka yi a kasar.

KU KARANTA: A kalla soji 13 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Boko Haram na kwanakin nan

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar Afirka ta kudu, Khusela Diko ya sanar a ranar Lahadi, ya ce, "Wakilan na musamman zasu mika sako daga shugaba Ramaphosa dangane da rikicin da ya barke a wasu sassan kasar, wanda ya zama sanadin harar 'yan kasashen ketare da ke kasar tare da barnatar musu da dukiya."

Ya kara da cewa, "Wakilan zasu kara tabbatarwa da kasashen Afirkan cewa kasarmu na nan rike da alkawarin hadin kai da kara na kasashen Afirka".

Kungiyar wakilan na musamman sun hada da: Jeff Radebe, Jakada Mbatha Mmabolo da Dr Khulu Mbatha wadanda zasu ziyarci kasashen Niger, Ghana, Senegal, Tanzania, Jamhuriyar Congo da Zambia.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel