Hukumar 'yan sanda sun cafke jami'in EFCC na bogi

Hukumar 'yan sanda sun cafke jami'in EFCC na bogi

- Hukumar 'yan sandan jihar Legas ta cafke wani sojan gona da sunan jami'in hukumar EFCC

- An cafkesa ne yayin da ya damfari wani mutum akan zai samarwa Dan sa aiki a hukumar

- Sojan gonan ya mallaki katin shaida na bogi da ke nuna shi jami'in hukumar ne

Yan sandan jihar Legas sun cafke wani mutum mai shekaru 29 da ake zarginsa da sojan gona a matsayin jami'in hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Wanda ake zargin mai suna Emeka Emmanuel 'yan sandan Ojo sun kamasa a ranar Asabar.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan, ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Kamar yadda Bala Elkana yace, an kama wanda zargin da laifin damfarar mutane ta hanyar musu alkwarin zai samar musu aiki a hukumar EFCC a matsayinsa na jami'in hukumar.

Wanda ya damfara na karshe mai suna Olaposi Semiu, wanda yayi wa Dan sa alkawarin samuwar aiki a hukumar bayan ya karba N51,000.

Wanda ake zargin ya mallakin katin bogi na shaidar zama jami'in hukumar wanda yake amfani da shi wajen damfara.

KU KARANTA: A kalla soji 13 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Boko Haram na kwanakin nan

Tuni wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

Bayan damfara, an kama wanda ake zargin da laifin da mallakar cibiyar lafiya a cikin gidansa.

"Sauran abubuwan da aka samu a gidansa sun hada da kayayyakin kiwon lafiya da shaidun karatu na bogi," inji 'yan sandan.

Hakazalika, an kama jami'an bogi na hukumar yaki da rashawa, EFCC a jihar Adamawa a ranar 4 ga watan Satumba. An kamasu ne bayan da suka damfari shugaban masu rinjaye, Hassan Barguma.

Wanda ake zargin mai suna Simon Bolki, ya sami shugaban masu rinjayen a ofishinsa inda ya bayyana masa katin shaidarsa na jami'in EFCC, kafin a kamasa.

Bayan kama jami'in bogin a jihar Legas, hukumar 'yan sandan jihar ta shawarci jama'a ballantana manema aikin yi da su kiyaye sakamakon yawaitar irinsu a gari.

'Yan sandan sunce ana cigaba da bincike kuma za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel