‘Yan Jihar Ebonyi za su samu aikin da babban bankin CBN - Kwamishina

‘Yan Jihar Ebonyi za su samu aikin da babban bankin CBN - Kwamishina

Mun samu labari cewa abban bankin Najeriya na CBN ya sha alwashin daukar wadanda su ka kammala jami’a da matakin digiri na farko a bangaren tattalin arziki a jami’a daga Ebonyi aiki.

Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto a Ranar 13 ga Watan Satumba, 2019, ainhin ‘yan jihar Ebonyi wadanda su ka kammala karatu da mafi kyawun sakamako za su samu shiga bankin CBN.

Kwamishinan jihar Ebonyi na yada labarai, Uchenna Orji, ya bayyana wannan a wata hira da yayi da Manema labarai bayan an kammala taron mako-mako na majalisar zartarwa ta jihar Ebonyi.

Kwamishinan yake cewa: “A sakamakon mu’amalar gwamna da CBN, bankin ya amince ya dauki kaf yaran jihar Ebonyi da su ka kammala jami’a da Digiri a fannin tattalin arziki aiki yanzu”

KU KARANTA: Abin da zai faru idan aka sake Makiyaya su ka tafi hutu a Najeriya

Wannan babban abu ne da ya kamata kowa ya yabawa a jihar, sannan kuma karin karfin gwiwa ne ga ‘Daliban mu da ke karatu da su kara himma domin samun irin wannan dama.” Inji Orji.

Kwamishinan ya kuma sanar da Manema labarai cewa gwamnatin jihar Ebonyi ta sa hannu da CBN wajen karbar wasu kudi Naira biliyan 2 da za ba ‘yan kasuwa da ma’aikata a matsayin bashi.

Yanzu duk yaron da ya tafi jami’a ya karanta harkar tattalin arziki a Najeriya ya kuma kammala da matakin farko na First Class, zai samu aiki da CBN muddin asalinsa ‘Dan jihar Ebonyi ne.

Orji yace za a raba wannan kudi ne da za a biya da karin ruwa na kashi 2% rak. Ma’aikatar tallafawa jama’a ce za ta sa ido wajen ganin yadda za a batar da wannan kudi wajen sana’o’i

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel