Takardun shaidar kammala karatu: Gwamnan APC zai kori ma'aikata 422 a jiharsa

Takardun shaidar kammala karatu: Gwamnan APC zai kori ma'aikata 422 a jiharsa

Gwamnatin jihar Osun ta umarci ma'aikatu da hukumominta a kan su gaggauta fara zartar da shawarar kwmitin da ya bayar da shawarar korar mutanen da suka samu aiki da takardun bogi ko kuma na aro.

Shugaban hukumar kwadago (NLC) a jihar, Jacob Adekomi, ya tabbatar da cewa lamarin zai shafi ma'aikata a kalla 422.

Ya ce saka bakin da kungiyar NLC ta yi ne ya kawo raguwar mutanen da za a kora zuwa 422 daga mutane 5,000 da gwamnatin ta yi niyyar kora tun farko.

A cikin wani jawabi da shugaban ma'aikatan jihar, Dakta Festus Oyebade, ya fitar ranar 13 ga watan Satumba, ya ce tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, ne ya dauko hayar wasu kwararru domin tantance takardun dukkan ma'aikatan gwamnatin jihar a shekarar 2015.

A cewar jawabin, "kwamitin kwararrun ya mika rahotonsa kuma gwamnatin baya ta amince da kaddamar da shi.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Yobe ta karbe wani filinta mai girman hekta 3.5 daga hannun rundunar soji

"Amma da sabuwar gwamnati ta hau mulki a watan Nuwamba na shekarar 2018, kungiyar kwadago ta roki gwamnatin da ta sake yin nazari a kan kaddamar da shawararin da kwararrun suka bayar."

A cikin jawabin, shugaban ma'aikatan ya kara da cewa tsoma bakin da kungiyar NLC ta yi ne yasa sabuwar gwamnatin jihar Osun a karkashin jagorancin, Gboyega Oyetola, ta kafa kwamiti mai mutane biyar domin sake duba shawarwarin da kuma zartar da su bisa daidai da tsarin dokokin aikin gwamnati.

"Bayan mun sake duba shawarwarin ne sai adadin mutanen da abin zai shafa ya koma 422, amma kungiyar NLC ta roki a sallame su kawai daga aiki ba tare da an gurfanar da su ko kuma an bukaci su dawo da albashi da alawus din da suka karba ba," a cewar Dakta Oyebade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel