Abin da kisan mabiyan mu zai haifar wa gwamnatin Buhari - Jigo a Shi'a

Abin da kisan mabiyan mu zai haifar wa gwamnatin Buhari - Jigo a Shi'a

Shugaban mabiya kungiyar IMN (Shi'a) da gwamnatin Najeriya ta haramta a jihar Gombe, Mallam Muhammad Adamu, ya bayyana kisan mabiyansu da jami'an tsaro ke yi a matsayin babban take hakkin bil'adama.

Da yake magana da manema labarai yayin binne gawarwakin wasu mabiya Shi'a da shugaban ya yi zargin cewa jami'an tsaro ne suka kashe shu, Adamu ya ce cigaba da kisan mambobinsu alama ce da ke nuna cewa karshen wannan gwamnati ya zo.

"Masu kashe mu basu basu san cewa mu na da mahalicci da zai yi mana sakayya ba a ranar gobe kiyama. Yanzu kam a bayyane take cewa gwamnati ba ta girmama doka. Duniya na kallo duk abin da yake faruwa na kisan mambobin mu a Najeriya.

"Mutane ma yanzu sun manta wanne zunubi mu ka aika wa gwamnatin tarayya. Cigaba da take hakkin mu kan iya zama wata alama da ke nuna cewa karshen wannan gwamnatin ya kusa zuwa. Mambobin mu su cigaba da yin addininsu kamar yadda suka yi imani" a cewar Mallam Adamu.

DUBA WANNAN: Samun nasara a kotu: Buhari bai yi 'mi'ara koma baya' a kan furucinsa ba - Fadar shugaban kasa

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne gwamnati ta haramta kungiyar Shi'a da duk wasu al'amuranta.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun kashe mambobin kungiyar Shi'a uku ranar Talata yayin da suka fito domin gudanar da tattakin 'Ashoura' a garin Gombe kamar yadda suka saba yi kowacce shekara.

Tun kafin ranar rundunar 'yan sanda ta gargade su a kan gudanar da tattakin amma mambobin kungiyar a jihohi da dama suka yi watsi da gargadin rundunar 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel