Keyamo zai biya kudin jinyar Magoya bayan APC da aka yi wa rauni a Delta

Keyamo zai biya kudin jinyar Magoya bayan APC da aka yi wa rauni a Delta

Karamin Ministan harkokin Neja-Delta a Najeriya, Festus Keyamo ya fito ya yi magana bayan ya samu labari cewa an kai wa wani Masoyin jam’iyyar APC hari a jiharsa ta Delta kwanan nan.

Wannan abu ya faru ne a Garin Effurun da ke cikin karamar hukumar Uvwie a jihar Delta inda wani Bawan Allah mai suna Elvis Omoiri ya kusa tafiya lahira saboda murnar nasarar APC a kotu.

Makwabacin Omori, Best Uduophori, ya daddatse shi ne bayan ya ji ya na murnar Muhammadu Buhari ya tika jam’iyyar PDP da kasa a shari’ar da aka yi na zaben shugaban kasa da aka yi bana.

Harin da aka kai wa wannan ‘dan gani kashe nin APC ya sa ya kusa rasa rayuwarsa. Mai girma Festus Keyamo ya nuna cewa za su yi kokarin ganin hukuma ta hukunta Best Uduophori.

Ministan na Neja-Delta yace ya aika Hadiminsa ya turo masa takardun asibitin wannan mutumi da ke kwance inda ya nuna zai dauki nauyin kudin da za a kashe wajen nema masa magani.

KU KARANTA: Minista Pantami ya zabi tsohon Ma’aikacinsa a matsayin sabon Hadiminsa

Bayan labarin ya ratsa gari, a jiya Asabar, 14 ga Watan Satumba, 2019, Kayemo ya ce: “Na shiga wannan maganar tun tuni. Na aika wani daga cikin Mukarrabai na zuwa wannan asibitin”

Ministan ya cigaba da cewa: “Na kuma ce a aiko mani lissafin kudin da ake bukata a asibitin. Na yi magana da wanda abin ya faru da shi, na kuma tabbatar masa da cewa za a dauki mataki."

Bayan haka sai na tuntubi babban jami’in ‘yan sanda na ofishin Ekpan domin tabbatar da cewa an kama wanda ya yi wannan mummunan aiki an hukunta sa. Inji Keyamo shafinsa na Tuwita.

Babban Lauya Keyamo ya yi wa APC aiki a matsayin Kakakin yakin neman zabe. Bayan nasarar da aka samu ne aka ba shi Minista. A makon jiya kuma APC ta samu nasara a kotun zaben 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel