Tabbas Buhari ya fi Atiku cancantar jagorancin Najeriya - APC reshen Arewa maso Gabas

Tabbas Buhari ya fi Atiku cancantar jagorancin Najeriya - APC reshen Arewa maso Gabas

Jam'iyyar APC reshen Arewa maso Gabashin Najeriya na taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara da yayi a kotun sauraron kararrakin zabe.

Reshen jam'iyyar ya ce nasarar da Buhari ya samu a kan dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, manuniya ce da ke tabbatar da cewa shi ya fi cancantar ya jagorancin kasar nan.

Da yake ganawa da manema labarai a babban ofishin jam'iyyar APC na kasa bayan zaman sulhu da fusatattun jam'iyyar dangane da abin da ya shafi babban zaben kasa na 2019, mataimakin shugaban jam'iyyar reshen Arewa maso Gabas, Kwamared Mustapha Salihu, ya ce hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta zartar, lamari ne da ko gizau ba su yi ba wajen sa rai da tabbatuwarsa.

Ana iya tuna cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne kotun sauraron kararrakin zabe, ta yanke hukunci a kan karar da Atiku ya shigar a gabanta, inda ya ke kalubalantar nasarar da shugaba Buhari yayi a babban zaben kasa na bana.

KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Babu sauran aminci a Najeriya - Wamakko

Kotun dai yayin zartar da hukuncinta a makon da ya gabata, ta yi watsi da karar tsohon mataimakin shugaban kasa, lamarin da ta ce shelar nasarar Buhari da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta yi ta gaskata.

Manyan Alkalan kotun biyar karkashin jagorancin mai shari'a Muhammad Garba, ta tabbatar ta sake tabbatar da nasarar shugaba Buhari a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairun 2019.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel