Allah Sarki: Alasoadura ya bada tarihin rayuwarsa tun yana boyi-boyi

Allah Sarki: Alasoadura ya bada tarihin rayuwarsa tun yana boyi-boyi

Sabon karamin Ministan kwadago, Tayo Alasoadura wanda ake ta magana a kan sa bayan jin labarin yadda rayuwa ta yi masa hallaci tun yana ‘Dan aike har ya zama babba ya bada tarihinsa.

Tayo Alasoadura ya yi wata doguwar hira da jaridar Daily Trust a jiya inda ya ce ya tashi ne a gidan Manoma, ya kuma zage wajen nema har ya yi karatun Boko ya kuma samu aikin yi.

Alasoadura ya ke cewa Iyayensa Manoma ne don haka kudin karatu ya gagare sa. A sanadiyyar haka ya rika noma masara da rogo a makaranta domin ya samu kudin karatu da na abinci.

Sabon Ministan ya karatu ne a makarantar Ajuwa Grammar School da ke Akoko a Ondo wanda wani ya yi masa hanya a lokacin. Yace ya kasance ya na aron litattafai ne daga hannun jama’a.

Sanata Alasoadura yace a haka Ubangiji ya yi masa gyadar doguwa ya rika hada karatu da noma har ta kai yana kwana a cikin gona, kuma ya yi dace ya ci jarrabawarsa fiye da sauran ‘yan ajinsa.

Kamar yadda Ministan ya ba ‘yan jarida labari, kokarinsa ya sa aka yi ta yi masa tsallake. Daga baya kuma yace ya samu wata kungiyar waje da ta rika tallafa masa da kudin karatu da abinci.

Alasodoura ya gamu da cikas ne bayan gama Sakandare, ya ci jarrabawa amma karatun gaba ya gagara duk da ya samu wata jami’a a kasar Amurka. Rashin kudin jirgi ya sa dole ya hakura.

KU KARANTA: Matasa sun yi wa Matar Sarki 'dan karen duka a Najeriya

Rashin iya zuwa jami’a a Amurka ta sa Alasodoura ya fara koyarwa a makaranta. Bayan ‘dan lokaci ya ajiye wannan aiki ya tafi wani kamfani ya na neman abin yi duk da bai san irin aikin ba.

Karamin Ministan kasar ya bada labarin yadda ya samu aiki a wannan kamfani wanda yanzu ake kira BBC inda yace ya yi dace ne kurum an dauke sa a matsayin mai dauko karafuna a cikin mota.

Sannu a hankali Tayo Alasoadura ya koma karatu ya samu shaidar ACCE inda zama Akawu bayan shekaru uku. Wannan ya sa aka kara masa matsayi da albashi a kamfanin da ya fara da ‘dan aike.

Da yake abu na Ubangiji ne, bayan shekaru goma, a shekarar 1978 Alasoadura ya ce ya zama Manajan wannan kamfani da yake aiki mai suna Balogun & Co. Daga nan rayuwar sa ta canza.

Tayo Alasoadura ya koma ya fara siyasa a gida har ya samu daukaka. A 2015 aka zabi Alasoadura a matsayin Sanatan Ondo ta tsakiya. Kwatsam sai aka ji cewa yanzu ya zama Ministan tarayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel