Dr. Isa Pantami ya nada Yusuf Abubakar a matsayin Hadiminsa

Dr. Isa Pantami ya nada Yusuf Abubakar a matsayin Hadiminsa

Mun samu labari cewa Ministan sadarwan Najeriya, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya fitar da wani sabon mukami. Ministan ya bada wannan mukami ne a cikin karshen makon nan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga ma’aikatar sadarwar kasar, Ali Ibrahim Pantami ya amince da nadin Yusuf Abubakar a matsayin Hadiminsa daga jiya Asabar 15 ga Satumba.

Mista Yusuf Abubakar zai zama Mai taimakawa Mai girma Ministan wajen harkokin yada labarai a kan kafafen sadarwa na zamani. Abubakar zai fara aiki ne ba da bata lokaci ba.

Mun fahimci cewa Yusuf Abubakar yana aiki ne a hukumar NITDA ta Najeriya a matsayin babban jami’in ta. Daga nan ne zai zo ma’aikatar sadarwa ya yi aiki da Ministan tarayyar.

Bisa dukkan alamu Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi aiki da Yusuf Abubakar lokacin ya na jagorantar hukumar ta NITDA inda ya baro bayan ya samu babbar kujerar Ministan Najeriya.

KU KARANTA: Ali Nuhu ya yi magana game da kamen da ake yi a Kannywood

Shekaru uku da su ka wuce ne shugaban kasa Muhammadu Buhari Pantami ya nada a matsayin shugaban NITDA. Yanzu Ministan ya karbi aron wani daga cikin tsohon Jami’an sa.

Abubakar shi ne zai rika kula da duk wasu harkokin sadarwa da watsa labarai a game da ma’aikatar ta kafafofin zamani irinsu Tuwita da Facebook da sauransu a karkashin Ministan.

Jama’a da dama dai sun fito su na taya Yusuf Abubakar murnar wannan babban mukami da ya samu. Dinbin mutane kuma a Tuwita sun yi Abubakar addu’ar Allah taya sa riko.

Idan ba ku manta ba a baya, Isa Pantami ya amince da nadin Inuwa Kashifu a matsayin Magajinsa a hukumar NITDA. Kashifu ya na cikin wadanda su ka yi aiki da Pantami.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel